31 Yuli 2026 - 22:08
Source: ABNA24
Ana Ci Gaba Da Tattakin Arba'een A Nijeriya + Hotuna

A jiya Alhamis 15 ga watan Safar 1448 (30/7/2026) 'yan uwa Musulmi almajiran Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) suka fara Tattakin Yaumul Arba'een din Imam Husaini (AS), daga Yankin Kano zuwa Zaria.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Tattakin, wanda ke misalta wahalhalun da iyalan gidan Manzon Allah (S) suka sha na jansu a kasa daga Kufa zuwa Dimashƙa bayan Waki'ar Karbala, ya hada da isar da sakon Mazlumiyar Ahlulbait (AS) ga al'ummar wannan nahiya.

'Yan uwa daga Da'irori daban-daban da ke jihohin Kano, Jigawa, Yobe, Maiduguri da sashin Bauchi (Azare) ne suke yi daga Yankin na Kano, wanda aka sa ran za su kai har zuwa ranar Lahadi suna gudanarwa.

Yankin Pambegua tuni suka fara Tattakin na Arba'een a safiyar yau Juma'a, su ma ana sa ran za su kai ranar Lahadi kafin su rufe.

Ga hotuna Tattakin na Yankin Kano da ya gudana a jiya.

OurMartyrsOurHeroes

15/Safar/1448

31/07/2027

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha